‘Yan Fashi Sun Sace Wani Darakta, Sun Nemi A Basu N40m Kudin Fansa A Kaduna

Gungun wasu mutane da ake zargin ‘yan fashi ne wadanda suka sace wani Darakta dake aiki a Ma’aikatar Ilimi, Kimiya da Fasaha ta Jihar Kaduna na neman a biyasu N40m kudin fansa, a cewar wani jami’in ma’aikatar

Wanda aka sacen mai suna Mr John Gorah, an sace shi ne da tsakar daren ranar Lahdi a gidansa dake Mararaban Rido a garin Kaduna.

Mataimakin Darakta a Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Mr Steven Haruna shi ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN a Kaduna ranar Talata cewa ‘yan fashin sun tuntubi iyalan wadanda suka sacen.

Haruna yayi bayanin cewa ‘yan fashin sun tsamma gidan mutumin, inda suka ringa harba bindiga sama don tsoratar da mutane suka kuma kayarda katangar gidan kafin su gudu da Gorah.

Ya kuma kara da cewa ‘yan fashin sun sace wata mata mai shayarwa makociyar mutumin, inda suka bar jaririnta dan sati uku da haihuwa.

“’Yan fashin sun kira iyalan mutumin suna neman a basu Naira Miliyan 40 kudin fansa,” kamar yadda ya fadawa kamfanin dillancin labarai na NAN.

418total visits,1visits today


Karanta:  An Gurfanar da Malamin Makaranta Saboda Zargisa da Lalata da ‘Yan Mata 3 ‘Yan Uwan Juna

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.