‘Yan Ghana Sun Yi Zanga-Zanga Kan Musgunawa Musulman Rohingya

Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda ake musguna wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya a Myanmar

Wasu daruruwan Musulmai a birnin Accra na kasar Ghana sun gudanar da wata kasaitaciyar zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu da cin zarafin da suka ce ake yi wa Musulmai ‘yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Masu zanga-zangar sun kuma nuna rashin jin dadinsu game da abun da suka kira ci gaba da sayar wa kasar makamai da kasar Israila take ci gaba da yi.

Sai dai, a dai dai lokacin da masu zanga zangar suke shirin shiga gari, sai ‘yan sanda suka dakatar da su.

Asalin Labari:

BBC Hausa

3217total visits,1visits today


Karanta:  Shugabar Gwamnatin Myanmar Ta Musanta Kisan Musulmi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.