‘Yan Kunar bakin wake sun kashe mutane 12

Wasu mata su biyu ‘yan kunar bakin wake sun hallaka mutane goma sha biyu (12), ciki har da yarinya, tare da raunata wasu guda arba’in (40) away wani dake daf da bodar Najeriya a arewacin kasar Kamaru.

Rahotanni sun bayyana cewar, matan wadanda suka aikata wannan mummunan aiki a ranar Laraba, sun kutsa kai cikin al’umma a garin Waza, wanda ke da tazarar kilomita takwas (8) daga bodar Najeriya.

Ma’aikata sun sanar da kamfanin dillancin labarai na AFP cewar “Maharan sun kai hari a wajen da ke cike da wajejen cin abinci, wajen buga wayar tarho da kuma wajen gudanar da sauran sana’oi”.

Bayyanai sun kara tabbatar da cewar, “Kafatanin garin a rufe yake, babu mai shiga babu mai fita. Hakazalika, wadanda suka samu rauni sakamakon harin na cikin mummunan hali”.

Har ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta fito ta amsa alhakin kai harin, amma yankin ya saba da ganin harin ‘yan kungiyar Boko Haram a yan shekarun nan.

 

 

 

Asalin Labari:

Aljazeera, Muryar Arewa

1742total visits,1visits today


Karanta:  Gwamnatin Nijar ta tsawaita dokar ta baci a yankin Diffa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.