‘Yan majalisa sun bukaci a rage kudin aikin hajji a Nigeria

Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta sayar wa maniyyata aikin hajjin bana da ta sayar musu da dalar Amurka kan naira 200, maimakon yadda Babban Bankin Kasar (CBN) yake sayar da ita a kan naira 305.

A ranar Laraba ne Sanata Adamu Aliero ya gabatar da wani kudiri a gaban majalisar yana zargin cewa CBN ya sayar wa wasu ‘yan kasuwa dala kan farashin naira 200.

Sai dai bankin ya musanta hakan.

Malam Abubakar Aliyu masanin tattalin arziki ya ce matakin ba zai shafi tattalin arziki kasar ba.

Farashin aikin hajjin ya kai kimanin naira miliyan daya da rabi.

Sai dai hukumar aikin hajjin kasar ta ce tashin farashin dala ne ya jawo tsadar farashin.

Asalin Labari:

BBC Hausa

762total visits,3visits today


Karanta:  An fara jigilar Alhazai a Nigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.