‘Yan Majisar Dokokin Jihar Niger Sunki Amincewa Da Bukatar Gwamna.

An ja layi tsakanin 'yan majilisar dokokin jihar Niger da Gwamna, domin ya nemi sun tantance wasu mutane 3 da yaso ya nada su masui bashi shawara amma sukace 15 din da yake dasu sun wadatar.

‘Yan Majilisar dokokin jihar Niger sunki amincewa da bukatar da Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya aike musu dashi na tantance wasu mutane 3 domin nada su amatsayin masu bashi shawara.

Wasu Bayanai sun nuna cewa majilisar ta dauki wannan mataki ne domin nuna rashin gamsuwa yadda gwamnatin jihar Niger ta kashe makuddan kudaden nan naira bililin dubu 7 da miliyan dari biyu na Paris Club da gwamnatin ta samo a kwanakin baya.

Honarabul Shaibu Liman Iya shine mai Magana da yawun majilisar dokokin.

‘’Duk abinda akayi da kudin, mu zamu zo mu sani tunda majilisa tana da matakan da zata bi na gudanar da ayyunta, idan aka bi ta ‘yan kwamiti na majilisa suka fita zasu bi dukkan maaikatu suka me akayi. Sannan masu baiwa gwamna shawara yanzun nan muna da kusan guda 15, inda yanzu an amince da guda 3 din nan kaga muna da 18 kenan to ai kaga ba karamin nauyi bane shi yasa muka ce a yanzun dai a dan saurara’’

‘Yan majilisar sunce suna cikin wani yanayi na talauci a sakamakon yadda aka dauki dogon lokaci ba tare gwamnatin jihar Niger ta basu kudaden su na gudanar da ayyukan mazabu ba.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1251total visits,1visits today


Karanta:  Osinbajo na shirin yin girgiza a Majalisar Zartarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.