‘Yan Nigeria na cikin ‘kunci’ bayan an korosu daga Bakassi

Wasu ‘yan Najeriya fiye da 300 na can suna zaman gudun hijira cikin wani yanayi da suka ce mawuyaci ne a jihar Kuros Ribas, bayan da suka tsere daga kasar Kamaru.

Sun samu kansu a cikin irin wannan hali ne bayan da suka tsere da kyar daga tsibirin na Bakassi, wanda Najeriyar ta mika wa kasar Kamaru a shekarun baya.

Masu gudun hijirar dai sun yi zargin cewa an kashe wasunsu da dama da suka hada da maza da mata, kuma an lalata masu gidaje da kadarori masu dimbin yawa a wani hari da jami’an tsaron kasar ta Kamaru suka kai masu.

Hakan ta wakana ne ga resu sakamakon rashin biyan wani haraji da suka ce an tsawwala masu.

Wata ‘yar gudun hijirar mai suna Mary Joseph da ta zo da tsohon ciki, ta shaida wa BBC cewa a yanzu tana da ‘ya ‘ya 10.

To sai dai har zuwa yanzu bata da kome a hannunta.

Mata da dama ne ke ta haihuwa a wannan sansani ba tare da wata kulawar da ta dace ba.

” Hatta ruwan sha babu ballantana maganar abinci, babu kuma kudin saye”.

Mr Linus Asuko masunci ne kuma daya daga cikin ‘yan gudun hijirar ya bayyana cewa yanzu ba su da komai, ga shi kuma gwamnatin Nijeriya ba ta yi musu komai ba, mutane na mutuwa.

Ya kuma ce ” Muna bukatar agajin gaggawa, muna bukatar tabarmi, da abinci, da magunguna, da gidan sauro, da kayan abinci, sannna a taimaka wa matan da ke haihuwa a wannan sansani.

Yan gudun hijira dai na fuskantar matsaloli daban-daban da suka hada da na rashin kudaden biyan bukatunsu, da wuraren kwanciya, da abinci da magunguna.

Karanta:  Yawancin Kananan Hukumomin Jahar Naija Na Cin Gashin Kansu.

Sai dai hukumomi a jihar ta Kuros Ribas sun ce suna kokarin tantance ‘yan gudun hijirar, da matsalolinsu, ta yadda nan ba da jimawa ba za a taimaka musu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

706total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.