‘Yan Nijeriya Na Bukatar Jam’iyyar PDP A Zaben 2019, Cewar Jonathan

Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya ce, ‘yan Nijeriya na bukatar jam’iyyar adawa ta PDP da ta dawo ta cigaba da mulkin kasar nan a shekarar 2019.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jiya Litinin yayin tattaunawar da shugabannin jam’iyyar su ka yi a babbar sakatariyyar jam’iyyar “Wadata Plaza” da ke Abuja.

Jonathan, ya bukaci jigogin jam’iyyar da su dinke barakar da ke tsakaninsu don hada kan ‘yan jam’iyyar da samun fahimta juna a tsakanin ‘yan jam’iyyar.

“Ina tabbatar mu ku da cewa, duk ‘yan jam’iyyar PDP da suka bar jam’iyyar sakamakon rikicin shugabanci za su dawo jam’iyyar” inji Jonathan.

Asalin Labari:

LEADERSHIP Hausa

585total visits,1visits today


Karanta:  Yemi Osinbajo ya yi 'kyakkyawar' ganawa da Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.