‘Yan Sanda Sun Koka Bisa Yawaitar Aikata Fyade a Kano

Jumimah Ayuba, shugabar sashin yaki da laifukan cin zarafin dan’adam da aikata Fyade na osfishin ‘yan sanda da ke Shahuci, ta ce babban abinda ke cewa jami’an tsaron tuwo a kwarya, shi ne yadda a mafi akasarin lokuta, kananan yara manya ke yi wa fyaden.

Jumimah ta kara da cewa ba da jimawa bane suka fara kokarin gurfanar da wani magidanci da ya yiwa ‘ya’yansa uku fyade, zalika sun kame wani mutum da ya yiwa jaririya ‘yar watanni 2 kacal a duniya fyaden.

A cewar jami’ar ‘yan sandan bincikensu ya nuna cewa daga cikin manyan dalilan da ke haddasa yawaitar fyaden, akwai, tallace-tallace, rashin nuna kulawar iyaye zuwa ‘ya’yansu, daukar kananan yara a matsayin masu aiki a gidaje, da kuma yawaitar samun mutuwar aure.

913total visits,3visits today


Karanta:  Aikin Hajji: Mahajjata 2 ‘Yan Kano Sun Mutu A Saudi Arabia

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.