‘Yan Sandan Najeriya Sun Jaddada Ci gaba Da Tsaron Lafiyar Al’uma Da Dukiyoyinsu

Wasu jami’an ‘yan Sanda dari bakwai da sittin da bakwai sun samun horo na masamman a cibiyar horar da dabarun shugabanci da zama dan kasa na gari a Shere Hill, dake birnin Jos.

Jami’an ‘yan Sandan masu matsakaicin mukamai daga kwalejin horar da ‘yan Sanda dake Jos, sun yi mako uku a cibiyar horar da dabarun shugabanci da zama dan kasa na gari inda suka samu horo akan matakai daban daban na kwarewa a aikin su da inganta dangantakarsu da al’uma.

Darakta a kwalejin horar da jami’an ‘yan Sanda dake Jos, D C Aminu Alhassan, yace horon da aka baiwa jami’an na ‘yan Sanda yana da mahimmanci kwarai, yana mai cewa dan Sanda yana cikin mutanen da ya kamata irin wannan horon saboda abune wanda zai sa mutun ya jurewa wahala da sai ya cimma abinda yake nema, saboda haka idan basu yi wannan ba yaya zasu sa wasu suyi ko kuma su jagorance su, ba za a samu nasara ba.

Shugaban cibiyar horar da dabarun shugabanci sa zama dan kasa na gari Abdulmumini Mamako, yace suna bada horo ne ta yarda al’uma zasu zama ‘yan kasa na gari, da kara inganta dangantakarsu da jama’a.

Asalin Labari:

VOA Hausa

3253total visits,2visits today


Karanta:  Taron nuna fasaha da al'adun gargajiya na Nahiyar Afrika a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.