‘Yan sandan Nigeria: ‘Evans yana nan bai mutu ba’

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa madugun da ake zargi da satar mutane Chukwuduneme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans bai mutu ba kuma jami'an tsaron kasar suna ci gaba da bincike a kansa.

Ta bayyana hakan ne bayan wasu kafafen yada labarai a kasar sun ruwaito cewa an kashe mutumin da ake zargi da satar mutane don neman kudin fansa.

Har ila yau, wasu rahotanni daga kasar cewa suka yi Evans ya tsire daga hannun jami’an tsaron kasar.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya Jimoh Moshood ya tabbatarwa BBC cewa “Evans yana nan da ransa a hannunmu.”

Ya ci gaba da cewa: “Batun da ke cewa Evans ya tsere ko kuma an kashe shi duka ba gaskiya ba ne. Ba zan iya bayyana muku inda da ake tsare da shi ba a halin yanzu saboda dalilan tsaro, amma har yanzu yana a hannunmu ne.”

Hakazalika, ya ce an yi nisa kan binciken da ake wa mutumin kuma za su gurfanar da shi a gaban kuliya “da zarar mun kammala bincike saboda laifukan da ake zarginsa da aikatawa suna da yawa,” kamar yadda ya ce.

“Mun samu izinin ci gaba da tare Evans har tsawon wata uku daga wata kotu,” in ji shi.

A watan jiya ne Evans ta hannun lauyansa ya shigar da rundunar ‘yan sandan kara a gaban wata babbar kotun kasar, inda yake zarginsu da tsare shi ba bisa ka’ida ba.

An cafke Evans ne a farkon watan Yuni a Legas tare da wasu mutum shida da ake zarginsu da satar mutane.

Asalin Labari:

BBC Hausa

563total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.