‘Yar arewacin Nigeria ta ci gasar Komla Dumor ta BBC ta 2017

Wata 'yar jarida daga arewa maso gabashin Najeriya ce ta lashe lambar yabo ta BBC ta Komla Dumor ta bana.

Amina Yuguda mai gabatar da labarai ce a gidan talbijin na Gotel da ke Yola, inda ta gabatar da labarai da dama har da wadanda suka shafi rikicin Boko Haram.

Za ta fara aikin koyon sanin makamar aiki na tsawon wata uku a London cikin watan Satumba.

An kirkiro lambar yabon ne don girmama Komla Dumor, wani mai gabatar da shiri a kafar yada labarai ta duniya ta BBC, wanda ya yi mutuwar farat daya a lokacin da yake da shekara 41 cikin shekarar 2014.

Amina Yuguda ta ce samun nasararta ‘babbar girmamawa ce.’

Asalin Labari:

BBC Hausa

2029total visits,2visits today


Karanta:  Amurkawa Na Murnar Aukuwar Kusufin Rana a Yau

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.