‘Yar shekara 59 ta rikida zuwa ‘yar shekara 30

Wata mata mai shekara 59 ta sa an yi mata kwaskwarimar sauya kamannun ta koma kamar mai shekaru 30 da doriya don boye wa masu binta bashi a birnin Wuhan da ke kasar Sin. Matar dai na fama da bashin Yuan miliyan 25 wato daidai da Dala miliyan uku da dubu 710, kamar yadda Kamafinin Dillanci labarai na Zinhua ya ruwaito

Wata mata mai shekara 59 ta sa an yi mata kwaskwarimar sauya kamannun ta koma kamar mai shekaru 30 da doriya don boye wa masu binta bashi a birnin Wuhan da ke kasar Sin. Matar dai na fama da bashin Yuan miliyan 25 wato daidai da Dala miliyan uku da dubu 710, kamar yadda Kamafinin Dillanci labarai na Zinhua ya ruwaito.

Al’am arin wannan mata na daya daga cikin matsalolin da ke ci wa kasar Sin tuwo a kwarya don haka ake kokarin kafa “kungiyar masu bashi,” a cewar Jami’an ’yan sanda wadanda rahoton da aka kai musu na karar wanan mata ya yi matukar ba su “mamaki,” bayan da suka kama matar, wadda tat sere zuwa birnin Shenzhen da ke Kudancin kasr bayan d akotu ta bayar da umarnin a kamota.

“Mun yi matukat mamakin,” a cewar rahoton jami’in Kamfanin Dillancin Labarai na dinhua, kamar yadda ya ruwkaito daga bakin jami’in ’yan sanda. “Ta yi kama da mai shekara 30 da doriya sabanin yadda take a hotunanta da aka ba mu. Matar dai mai suna Zhu Najuan, ta dai amsa laifinta, inda ta yi ikrarin amfani da katin hada-hadar kudi na mutane wajen yin tafiye-tafiye ta jirgin kasa a daukacin fadinb kasar. Ta kuma biya kudin aikin kwaskwarimar gyaran jiki da sauyin fuskar da aka yi mat ane da kudin da ciwo bashinsu daga banki, kamar yadda dinhua ya ruwaito.

Wakilan al’umma da suka fito daga birane fiye da 300 sun yi kudurin tun cikin Yilin bana cewa za su samar da rance ga masu hada-hadar sayen kayayyaki, ta yadda kasar za ta kara bunkasa tattalin arzikinta, ta kuma rage dogaro da jarin masana’antu wajen samar da kayan more jin dadin rayuwa.

A cewasr kamfanin dillancin labarai wata kotu a Lardin Jiangsu ta jero sunayen masu dimbin bashi da za a daina ta’ammali da su. An ce duk wanda sunansa ya bayyana a jerin sun ayemn idan ya kira lambar tarho din mutum sai a dauki maganarsa,” inda za a bukaci ya cika duk wasu ka’idoji na doka da suka rataya akansa.

Karanta:  Gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijirar Syria
Asalin Labari:

Daily Trust

409total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.