Yawancin Kananan Hukumomin Jahar Naija Na Cin Gashin Kansu.

A cigaba da rigimar da ake yi kan ba ma kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu musamman ma game da abin da ya shafi asusunsu, gwamnan jahar Naija ya ce shi kam a shirye ya ke ya ba su 'yancin.

A yayin da kananan hukumomin wasu jahohi ke ta korafe-korafe saboda hana su cin gashin kansu, gwamnan jahar Naija ya ce akasarin kananan hukumomin jaharsa na cin gashin kansu ne dangane da batun asusu. Ya ce kananan hukumomin da ba su iya tsayawa da gindinsu ne kadai har yanzu ke da asusun hadaka da gwamnatin jahar saboda a karfafa su.

Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce idan da ta shi ne da kowace karamar hukuma na cin gashin kanta a jahar; to amma wasu kananan hukumomi 12 a jahar sai an tallafa masu saboda ba su da kudaden shiga sosai. Ya ce duk wata jahar da ke da karfen tsayawa da gindinta an barta ta ci gashin kanta. Ya ce daya daga cikin matsalolin irin kananan hukumomin shi ne yawan ma’aikata da su ka dauka wanda hakan ya sa ko albashin ma’aikata ba su iya biya.

To saidai Gwamna Bello ya ce idan ana so ne a bai wa kananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kai, to ya kamata a bas u tare da irin nauyin da ke tattare da cin gashin kai din. Y ace bai kamata a ware masu asusu sannan kuma a dora ma jaha nauyin bayan albashin malaman makaranta ba.

Asalin Labari:

VOA Hausa

327total visits,1visits today


Karanta:  Dangote Zai Gina Katafaren Kamfanin Siga a Jihar Neja

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.