Za a ba ‘yan Boko Haram da suka mika wuya horo

Hukumomi a Najeriya sun ce za su fara ba wasu ‘yan Boko Haram 43 da suka mika wuya horo kan yadda za su gyara dabi’ansu.

A wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin kasar Kanar Onyema Nwachukwu ya aiko wa BBC, ya ce: “Mayakan Boko Haram 43 da suka mika wuya an kai su jihar Gombe don a hada su da sauran wadanda suka mika wuya saboda fara ba su horo kan gyaran halayya.”

Har ila yau, rundunar sojin ta ba da tabbacin cewa mayakan da suka mika wuya za su samu kyakykyawar rayuwa bayan kammala horon.

Hakazalika, rundunar ta bukaci sauran mayakan kungiyar da su yi watsi da kungiyar kuma “suma su mika wuya ba tare da bata lokaci ba,” kamar yadda ta ce.

Asalin Labari:

BBC Hausa

523total visits,2visits today


Karanta:  Gwamnati Ta Dukufa Wajen Ceto Mutanen Da Aka Sace a Borno - Osinbajo

Leave a Reply

Your email address will not be published.