Za a Kai Gwamnatin Taraba kotun ICC

 

Wani babban Laura Farfesa Yusuf Dankofa tare da kungiyar Miyatti Allah sun bayyana cewar za su maka Gwamnatin Taraba a kotun hukunta laifukan yaki ta duniya bisa zargin hannu a kisan kiyashi da aka yi wa fulani a Mambila dake jihar.

A wata hira da yayi da sashen Hausa BBC, Farfesa Yusuf Dankofa yace suna da shaidar cewa gwamnan jihar da kakakin majalisar sun yi kalaman da suka tunzura mutane, wanda hakan ya kai kisan kiyashin da aka yi wa fulani.

A ‘yan makonnin da suka gabata ne dai aka yi ta samun rikici mai nasaba da kabilanci tsakanin Fulani da Mambilawa.

Alkaluman da ba na gwamnati ba sun nuna mutane kimanin duba daya sun mutu sannan an kashe dabbobi fiye da dubu uku. Sai dai a wani martani da gwamnatin ta fitar ta bakin Kwamishinan Yada Labaran Jihar Anthony Danburam ya musanta duka large-zargen, yana mai cewa babu hannunsu a ciki.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, BBC Hausa

1125total visits,1visits today


Karanta:  Wata Cuta da Ba'a Tantance Ba Ta Hallaka Daruruwan Shanu a Jihar Filato (Jos)

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.