Za a kara yawan haruffan sakon Twitter

Hukumar shafin sada zumunta da muhawara na Twitter ta ce tana duba yuwuwar kawo karshe takaita yawan haruffan da masu amfani da shafin ke yi na iya haruffa 140, inda za ta linka yawan biyu.

Daya daga cikin wadanda suka kirkiro shafin na Twitter kuma babban shugabansa, Jack Dorsey, ya ce, rubutun da masu amfani da shafin suke yi zai ci gaba da zama dan takaitacce, amma dai yawan haruffan zai iya linkawa biyu, zuwa haruffa 280, a sako daya nan gaba.

Tuni dai aka fara wannan gwaji a tsakanin wasu masu amfani da shafin, ‘ya kadan.

Sabon tsarin dai na nufin fitattu daga cikin masu amfani da Twitter din, kamar Shugaba Donald Trump na Amurka, a yanzu za su samu karin damar bayyana ra’ayinsu cikin sauki.

A wani sako da kamfanin ya fitar game da shirin ya ce, ya fahimci cewa, dadadden tsarin takaita haruffan, abu ne da ya dade yana ci wa wasu mutanen tuwo a kwarya.

Sannan ya ce shi kansa shafin yana fama da matsalar rashin bunkasa yadda ya kamata, saboda haka, sauyin zai iya kasancewa wata hanya da shi kansa zai burunkasa, ya kuma samu sabbin masu amfani da shi.

Daya daga cikin manyan jami’an kamfanin shafin na Twitter Aliza Rosen, ta ce su kansu suna jin yadda abin yake da wuya da bacin rai, yadda za ka yi ta kokarin dunkule sakonka cikin ‘yan wadannan haruffa 140.

Jami’ar ta ce sun jarraba sabon tsarin, sun ga irin tasirin da zai yi, suka ga ya dace, duk da cewa shi ma dai takaitacce ne.

Wasu dai na ganin irin yadda ake samun karuwar damuwa a kan yawan kalamai na batanci da kyama da farfaganda da makamankansu, me zai sa shafin na Twitter ya tashi tsaye wajen ganin ya linka yawan haruffan da ake rubuta sakonni da su a cikinsa.

Asalin Labari:

BBC Hausa

465total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.