Za A Sabunta Wa’adin Kama Shekau

Da alamar dai duk da bugun kirji da Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi cewa an kasa kama shi cikin wa'adin da aka bayar, tsugune ba ta kare masa ba, saboda ko rundunar sojin Najeriya ta ce ta na tunanin sabunta wa'adin.

Bayan cikar wa’adin kwanaki 40 na kama shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ba tare da hukumar sojin Najeriya ta yi nasarar kama shi, kamar yadda Babban Hafsan Sojin Najeriya Janar Yusuf Burutai ya umurta ba, hukumar sojin ta ce dama wa’adin wani jadawali ne na tayar da azamar kama Shekau, saboda haka rashin kama Shekau cikin wa’adin da aka gindaya ba ya nufin shikenan an kawo karshen kama Shekau. Ta ce za a sabunta wannan wa’adin a kuma cigaba da kokarin kama Shekau.

Babban kwamandan rundunar “Operation Lafiya Dole” mai yaki da Boko Haram, wanda ya yi karin bayani, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya ce a yanzu an sa batun kama Shekau na kan gaba. To amma wani tsohon hafsa a hukumar leken asirin Najeriya, Aliko Arrashid Harun yace dama bai kamata a rika bayyana matakin soja mai sarkakkiya ba sai bayan an aiwatar kafin a rika cewa dama an shirya yin hakan ne.

Tsohon jami’in tsaron y aba da misali da yadda Amurka kan sakaya muhimman sojan da ta ke daukawa har sai ta yi nasara kafin ta kuma shiga bayanin cewa dama ta tsara hakan ne. Ya ce Amurka ta shafe shekaru shida ta na kokarin kama marigayi Usama bin Ladan ba tare da gaya ma duniya ddabarunta na kamawa ko kashe Bin Ladan ba.

Asalin Labari:

VOA Hausa

851total visits,1visits today


Karanta:  "An yi wa Fulani kisan-ƙare-dangi a Taraba"

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.