Za a sasanta Sarkin Musulmi da dan uwansa

An fara sulhunta wani sabani da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad a Najeriya da daya daga cikin manyan 'yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba.

A ranar Litinin ne dai magajin gari ya fice a fusace daga wani zaure da suke ganawa da Sarkin kuma ya sanar da yin Murabus daga kan mukamin wanda ya rike tsawon shekara 20.

Magajin garin dai ya yi zargin cewa sarkin ya ci masa zarafi a wajen wani sulhu da ake tsakaninsa da wani da sarkin ke son bai wa wata sarauta, amma masarautar ta ce ya yi hakan ne saboda sarkin ya ki amincewa ya sa baki kan wata matsala da ke tsakanin kamfaninsa da Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati (EFCC).

Ana tattaunawar sulhun ne bayan da wasu manyan sarakuna a kasar suka shiga tsakanin bangarorin biyu ciki har da Sarkin Gwandu Alhaji Muhammad Iliyasu Bashar da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu.

Har ila yau, BBC ta tuntubi Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba kuma ya tabbatar da cewa ana ci gaba da sulhunta su.

A ranar Asabar ne za a yi wani taro a masarautar don kammala sasanta bangarorin biyu, wanda wasu manyan sarakuna za su halarta.

Sai dai akwai bayanan da cewa har yanzu ba a kammala tattaunawar ba tukuna.

Ba a saba ganin takaddamar a marautar Sokoto ba.

Sarautar Magajin Gari shi ne na uku a jerin masarautar Sokoton.

Asalin Labari:

BBC Hausa

597total visits,1visits today


Karanta:  Jirgin Saman Ethiopian Zai Fara Jigila Daga Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.