Zaben Jamus: Angela Merkel Ta Lashe Wa’adi Na Hudu

Sakamakon binciken yadda mutane suka yi zabe yau a Jamus, ya yi hasashen jam'iyyar shugaba Angela Merkel mai ra'ayin gargajiya, za ta ci gaba da zama mai rinjaye a majalisar dokokin kasar.

Sai dai sakamakon ya nuna dukkan jam’iyyun, sun samu raguwar magoya baya fiye da a kowanne lokaci.

An yi hasashen jam’iyyar Christian Democratic Union ta Mrs Merkel, da CSU ta Bavaria wacce ra’ayinsu ya zo daya, sun lashe kashi talatin da uku cikin dari na kuri’un da aka kada.

Hasashen ya nuna babbar jam’iyyar hamayya ta ‘yan gurguzu, Social Democrats, ta samu kashi ashirin cikin dari na kuri’un.

Ana gani jam’iyyar da bata son baki, ta masu tsananin ra’ayin gargajiya ce za ta zo ta uku, da kashi goma sha uku cikin dari na kuri’u.

Ana gani jam’iyyar ta lashe wasu kujeru a majalisar dokokin kasar a karo na farko.

Shugaba Angela Merkel ta ce ta so a ce sakamakon da jam’iyyar ta, ta samu, yafi haka kyau, sannan ta ce za ta yi nazari game da damuwar wadanda suka zabi jam’iyyar da bata son baki, AFD.

Ta ce sun yi shekara 12 muna gudanar da shugabanci, kuma hakan ya sa jam’iyyar mu ta sake zama mafi girma. Sai dai za mu yi kokarin samun goyon bayan wadanda suka kada ma AFD kuri’a, musanman yayin da muke son bullo da muhimman manufofi.

Shugabar jam’iyyar AFD, Frauke Petry, ta ce abin da ‘yan kasar ta Jamus suka gani yanzu, wata girgizar kasa ce ta siyasa.

Daya daga cikin manyan ‘yan takara biyu na jam’iyyar, Alexander Gauland, ya ce sun yi wa Mrs Merkel shiri sosai na kwato abin da ya kira kasar su.

Shugaban jam’iyyar Social Democrats, Martin Schulz, ya amsa cewa sun sha kaye, yana mai cewa wannan rana ce ta bakin ciki.

Karanta:  Wanene sabon yariman Saudi Arabia?

Ya ce zai ci gaba da yin jagorancin jam’iyyar, tare da kawo mata sauye-sauye, amma dai ba za su shiga gwamnatin hadaka da Mrs Merkel ba.

Asalin Labari:

BBC Hausa

750total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.