Zakarun Nahiyoyi: Kamaru ta yi 1-1 da Australia

Kamaru ta yi kunnen doki 1-1 da Australia a gasar cin kofin zakarun nahiyoyi da ake yi a Rasha a ranar Alhamis din nan.

Zakarun na Afirka su ne suka fara jefa kwallo a raga ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, ta hannun Zambo Anguissa.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokacin ne kuma a minti na 60, Austalia ta rama da bugun fanareti wadda Milligan ya ci mata.

Wasan shi ne wasa na biyu tsakanin kungiyoyin a rukuninsu na biyu (Group B).

Kafin haduwar Jamus da Chile nan gaba a ranar Alhamis din nan

Chile ce ta daya a teburinsu da maki uku da kuma kwallo biyu a wasa daya.

Sai Jamus tana bi mata baya ita ma da maki uku amma da kwallo daya a wasa daya.

Australia ce ta uku da maki daya, sai bashin kwallo daya a ragarta, yayin da Kamaru take ta karshe da maki daya da kuma bashin kwallo biyu a ragarta.

A ranar Lahadi za a yi wasan karshe na rukunin na biyu, inda Kamaru za ta kara da Jamus, ita kuma Australia ta hadu da Chile.

Kafin sannan ‘yan rukunin farko za su gama wasansu ranar Asabar, inda Rasha mai masaukin baki za ta hadu da Mexico, New Zealand ta fafata da Portugal.

Daga nan ne kuma za a samu kungiyoyi hudu da za su yi wasan kusa da karshe na gasar

601total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.