Zama lafiya a Nigeria muke addu’a kullum – Buhari

Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya nemi al’ummar ƙasar su guji maganganun tayar da hankali, su rungumi zaman lafiya da juna.

Ya ce “zama lafiya a Nijeriya, shi muke roƙon Allah kullum.”

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a cikin saƙonsa na bikin ƙaramar sallah, karon farko bayan kwana 48.

Wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza ya ce ga alama shugaban na bayani ne game da musayar kalaman nuna ƙiyayya “tsakanin wasu ɓangarori na Nijeriya”.

A iya fahimtata saƙon sahihi ne, murya ce ta shugaba Muhammadu Buhari kuma murya ce wadda ta nuna an naɗe ta, ba da jimawa ba, in ji Tangaza.

Ya ce don kuwa ta yi bayani kan wasu batutuwa da ake ciki, da suka haɗar da bikin sallah da kuma damuna gami da uwa-uba kalaman nuna ƙiyayya.

A baya- bayan nan dai, Muƙaddashin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi ta gudanar da taruka da wasu fitattun mutane da sarakuna don kwantar da ƙurar da ta taso.

Dambarwa ta ɓarke ne lokacin da wasu ƙungiyoyin matasa a arewacin ƙasar suka ba ‘yan ƙabilar Igbo wa’adi na su fice daga yankin.

A cewarsu, saboda ƙaruwar kiraye-kirayen da wasu ƙungiyoyin Igbon ke yi don neman kafa ƙasar Biafra a yankin kudu maso gabas.

Lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce da tankiya har ma da musayar ba da wa’adi a tsakanin wasu ‘yan ƙasar.

A cikin jawabin, Buhari ya gode wa ‘yan Nijeriya kan yadda suke yi masa addu’o’in samun lafiya.

Ya kuma yi fatan saukar damuna mai albarka don samun abinci cikin sauƙi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

572total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.