Zaman Lafiya Ya Dawo A Birnin Aba.

Zaman lafiya ya dawo a jihar Abia inda aka kwashe kwanaki ana zaman dar-dar, wannan ne ma yasa Hausawa mazauna jihar suka bukaci 'yan uwansu da suka wuce Arewacin Kasar da su dawo.

Bayanai sun tabbatar da cewa yanzu an samu zaman lafiya a birnin Aba, inda aka kwashe makonni ana samun tashe-tashen hankula.

Wannan ne yasa har wasu Hausawa suke kira ga ‘yan uwan su da suka arce zuwa arewacin Nigeria da su dawo.

Yanzu haka dai jamia’an tsaro sun wadata cikin birnin na Aba, kuma harkoki sun koma yadda suke sai dai abinda ba a rasa ba.

Asalin Labari:

VOA Hausa

194total visits,1visits today


Karanta:  Mijina Mashayin Giya Ne Don Haka A Raba Auren Mu, Wata Mata Ke Fadawa Kotu

Leave a Reply

Your email address will not be published.