Zamu Cigaba Da Gwajin Makamanmu – Jong-Un

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya yi alkawarin gwajin Karin makamai masu linzami ta kan sararin samaniyar Japan, yana mai cewa gwajin baya somin tabi ne.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito shugaban na cewa nan gaba za a samu karin gwaje-gwajen makamai masu linzami, tare da danganta gwajin da suka yi a ranar talata a matsayin shirin yadda za a murkushe Guam domin mayar da martini ga atisayen da sojin Amurka da Koriya ta kudu ke yi.

Wannan shi ne karo na farko da Koriya ke amincewa da harba makaminta kan kasar Japan.

A ranar Talata ne Koriya ta arewa ta yi cilla makaminta mai linzami da ya ratsa arewacin Japan, matakin da ya dada kara haifar da fargabar barkewa yaki tsakanin kasar da Amurka.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi allawadai da matakan na Koriya ta arewa, wanda ta kwamitin tsaro ya danganta a matsayin barazana ga duniya.

Asalin Labari:

RFI Hausa

4374total visits,1visits today


Karanta:  Angola - Jam'iyyar MPLA ta Lashe Zaben Shugabancin Kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.