Zamu tabbatar harkar lafiya ta samu isassun kudi a 2018 – Saraki

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dakta Bukola Saraki ya bayyana cewa Majalisar Dattawan zata yi iya bakin kokarin don ganin cewar fannin lafiya ya samu isassun kudade a kasafin kudin badi.

Shugaban ya ambata hakan a lokacin bude taron karawa juna ilimi akan harkar lafiya a bangaren zartaswa. Shugaban ya kara da cewa ya umarci ministan lafiya daya sanarwa da bangaren zartaswa na majalisa adadin kudaden da bangaren lafiya ke bukata ga kowanne dan kasa.

Da yake jawabi a wajen taron Datka Saraki ya bayyana cewa akwai kungiyoyi da dama da suka hada da masu zaman kansu da kuma na kasashen ketare wadanda suke bukatar hada kai da bangaren zartaswar domin ganin an cimma gudanar da harkar lafiya.

Sakari wanda ya kasance kusa a yayin bude taron ya shaida cewa “idan har fannin lafiya ya shafi bangarori da suka hada da Malariya, allurar riga kafin yara da bangaren masu juna biyu to lallai Najeriya zata zama ta warware kusan dukkanin matsalolin bangaren lafiya.

Dakta Saraki ya cigaba da cewa a lokacin da gwamnatin Kwara ta tsayakai da fata wajen tabbatar da samar da lafiya ga al’ummar jihar, sun hada kai tare da kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen ketare da kuma na gida, wanda tare da hadin kansu ne, mutane da dama suka sami shiga cikin tsarin bai daya da fannin lafiya akan kudi da bai gaza Naira dari uku ba (N300).

894total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.