Ga aikin da zai iya samar da sama da naira miliyan uku a wata

Shin kun san gina manhajar kwamfuta mai farin jini ka iya samar wa mutum akalla dala dubu goma, wato sama da naira miliyan uku kowane wata?

Ga aikin da zai iya samar da sama da naira miliyan uku a wata

Wannan na cikin albishir din da Zubairu Dalhatu Malami, wani dan Najeriya mai kamfanin sadarwar intanet da ke hulda da kamfanin Google, ya yi wa matasan Najeriya. Zubairu ya ziyarci ofishinmu na London ne bayan ya halarci wani taron da kamfanin Google ya shirya wanda aka yi wa lakabi da ‘Google Cloud Next’ da zummar […]

An daure ‘yan makaranta kan wasa da Boko Haram

Wata sanarwar da Kungiyar Amnesty International ta fitar ta ce Jami'an tsaro sama da goma sun rufe dakin taron da ke wani otal a Yaunde, babban birnin Kamaru domin hana taron manema labarai da zai yi kira a saki 'yan makarantar da aka daure kan laifin rashin "yin tir da ayyukan ta'addanci."

An daure ‘yan makaranta kan wasa da Boko Haram

An kama yaran ne bayan an samu wanin sakon tes a wayoyinsu na salula game da kungiyar masu tada kayar baya ta Boko Haram. Sakon tes din da aka samu wayoyin ‘yan makarantar dai yana raha ne kan Boko Haram da kuma wuyar samun aiki a Kamaru. “Boko Haram na daukar mutanen da suka dara […]

Hare-haren intanet; da sauran rina a kaba

Hare-haren intanet; da sauran rina a kaba

Harin manhajar da ya shafi kasashe 150 ya fara raguwa, amma an sami rahotannin sabbin hare-hare daga nahiyar Asiya da Turai a ranar Litinin. An yi kira ga ma’aikata da za su koma bakin aiki a ranar Litinin din, da su yi tsantseni wajen amfani da na’uraorin komfutarsu. Wannan manhajar ta WannaCry ta fara bazuwa […]