Gwamnonin Arewa Na So a Ja Kunnen Nnamdi Kanu

Gwamnonin Arewa Na So a Ja Kunnen Nnamdi Kanu

Gwamanonin arewacin Najeriya sun yi kira ga takwarorinsu na kudu maso gabashin kasar, da su tsawatar shugaban kungiyar masu fafitikar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu kan irin kalaman da yake yi. Shugaban kungiyar gwamnonin na arewa, gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima shi ne ya yi wannan kira yayin wata hira da yi da Muryar Amurka […]

An kama ”yan luwadi 42′ a Legos

An kama ”yan luwadi 42′ a Legos

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a Najeriya ta ce ta kama wasu maza guda 42 da ake zargi da luwadi. An dai kama mutanen ne a wani otal, bayan da rundunar ta kai wani samame sakamakon samun bayanan sirri kan abun da mutanen ke aikatawa. Yanzu haka rundunar ta ce za ta gurfanar da su […]

Cristiano Ronaldo ya gurfana a gaban kuliya kan haraji

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya bayyana a gaban kuliya nan gaba a birnin Madrid domin ya bayar da bahasi kan tuhumar sa da ake yi da zamba cikin aminci wajen biyan haraji.

Cristiano Ronaldo ya gurfana a gaban kuliya kan haraji

Masu shigara da kara dai na zargin Ronaldo, wanda shi ne mai rike kanbun gwarzon dan kwallon duniya, da kin biyan harajin da ya kai dala miliyan 17. Sai dai kuma dan kwallon ya yi watsi da wannan zargi. Idan dai har aka samu dan wasan dan asalin kasar Portugal da laifi kan abin da […]

An tarwatsa taron APC a Kaduna

An samu hatsaniya a sakatariyar 'yan jarida da ke jihar Kaduna yayin da wasu sanatocin jam'iyyar APC ke taro da manema labarai, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

An tarwatsa taron APC a Kaduna

“Wadansu mutane ne dauke da makamai suka kai hari cibiyar ‘yan jarida da ke kan hanyar Muhammadu Buhari Way (Waff Road) ranar Lahadi,” a cewar rahotanni. Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hukunyi da kuma wasu ‘yan siyasa jihar ne suka kira taron manema labaran. “Yau (Lahadi) a sakatariyar ‘yan jarida da ke Kaduna muna […]

An fara jigilar Alhazai a Nigeria

An fara jigilar Alhazai a Nigeria

Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta ce ta fara jigilar maniyya aikin hajjin bana a Najeriya inda alhazai suka fara tashi daga shiyyar Abuja ranar Lahadi. Shugaban hukumar Abdullahi Muktar ya shaida wa BBC cewa “an yi sahun farko daga Abuja inda aka kwashe alhazai 480 da misalin karfe 3:16 na ranar Lahadi.” Ya ce ana […]

Sojin Nigeria sun amsa yin kuskure kan harin Borno

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana alhininta game da harin da kungiyar Boko Haram ta kai wanda ya zama saniyyar mutuwar ma'aikatan da ke binciken mai a gundumar Borno Yesu ta karamar hukumar Magumeri dake jihar Borno.

Sojin Nigeria sun amsa yin kuskure kan harin Borno

Ma’aikatan da suka rasa rayukansu sun hada da ma’aikatan kamfanin mai na kasa, NNPC, da wasu ma’aikatan jami’ar Maidugui har da da sojojin da ke raka su tare da ‘yan kato da gora. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin Najeriya, Birgediya-Janar Sani Kukasheka Usman ya sanya wa hannu, rundunar sojojin ta ce abin […]

Ahmed Makarfi Yayi Hadarin Mota

Ahmed Makarfi Yayi Hadarin Mota

Shugaban rikon kwarya na Jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, Sanata Ahmed Makarfi ya tsallake wani hadarin mota a jiya (29 July 2017) a hanyar sa ta zuwa jihar Kaduna daga babban birnin tarayya Abuja. Wata majiya ta bayyana cewa motar Sanata Makarfi tayi karo da wata mota a kan babban titin na Abuja zuwa Kaduna. […]

Najeriya Zata Iya Kawar Da Cutar Hanta Kwata Kwata Zuwa 2030

Ranar yau ce ranar tunatar da jama'a illar ciwon cutar Hanta a duniya kuma taken bana shine “Kawar da cutar Hanta daga doron kasa”.

Najeriya Zata Iya Kawar Da Cutar Hanta Kwata Kwata Zuwa 2030

Yau ranar ce da majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar cutar ciwon Hanta ta duniya wacce ake kira Hepatitis, bisa kididdigar da hukumar kula da lafiya ta duniya ta bayar akwai akalla mutane biliyan biyu masu dauke da cutar Hanta a fadin duniya, wanda daga ciki akalla mutane miliyan biyu na mutuwa sanadiyar […]

Ashley Fletcher: Middlesbrough ta sayi dan wasan West Ham

Ashley Fletcher: Middlesbrough ta sayi dan wasan West Ham

Middlesbrough ta sayi dan wasan gaban West Ham United, Ashley Fletcher, a yarjejeniyar shekara hudu kan Fam miliyan 6.5. Fletcher, mai shekara 21, ya bar sansanin atisayen Hammers a Jamus ne ranar Alhamis domin som tattaunawa da kungiyar da ke gasar Championship. Kawo yanzu Boro ta kashe kimanin Fam miliyan 30 kan ‘yan wasan gaba […]

1 2 3 23