Yadda fasto ya kare Musulmi 2000 a cocinsa

Wani limanin cocin katolika a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ya bai wa wadansu Musulmi su 2000 mafaka lokacin da suke cikin fargabar fuskantar hari daga kungiyar gwagwarmayar Kristoci ta anti-Balaka.

Fasto Juan José Aguirre Munoz ya ce Musulmin ‘yan gudun hijiran ba za su bar harabar cocinsa ba a birnin Bangassou da ke kudu-maso-gabashin kasar, sai bayan ya samu tabbaci kan tsaron rayukansu. Ya ce Musulmin da ya ba mafaka suna “fuskantar barazanar kisa” ne daga wurin mambobin kungiyar anti-Balaka. Wani babban jami’in Majalisar Dinkin […]

Mene ne hukuncin daukar hoto a wuraren Ibadah?

Daukar hoton a wuraren ibada abu ne da mutane suke yawan yi kuma su wallafa hotunan a shafukan sada zumunta na zamani inda abokansu za su gani su kuma yi tsokaci ko magana ko kuma yayata hoton.

Mene ne hukuncin daukar hoto a wuraren Ibadah?

Ba sabon abu ba ne mutun ya dauki hoto a masallacin idi ko na harami a Makka ko Madina ko kuma a filin Arfa. Bugu da kari wasu na daukar hotuna na bidiyo a lokacin dawafi ko kuma lokacin hawa Arfa kuma su wallafa a shafukan sada zumunta na zamani. Wata kila wasu na yin […]

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Hada Jihohi Uku da Layin Dogo

Ministan sufuri Amaechi ya fada a Sokoto gwamnatin tarayya na shirin hada jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto da layin dogo irin na zamani

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Hada Jihohi Uku da Layin Dogo

Kokarin gwamnatin tarayyar Najeriya na hada jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto da layin dogo ba zai tabbata ba sai da amincewar Majalisar Dattawa a cewar ministan sufurin kasar. A cewarsa tuni gwamnati ta tura bukatar zuwa majalisar. Rotimi Amaechi wanda shi ne ministan sufuri a karkashin shugabanci Muhammad Buhari yace jihohin uku da ake son […]

Takaddamar cinikin ranar karshe da aka yi a Premier

A ranar Alhamis 31 ga watan Agusta za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa ta Turai ta bana, wacce za a sake budewa a watan Janairun 2018.

Takaddamar cinikin ranar karshe da aka yi a Premier

Ana bude kasuwar ce domin bai wa kungiyoyin Turai damar daura damarar tunkarar kalubalen tamaula a sabuwar kaka. Ga jerin cinikin ranar rufe kasuwar da aka yi takaddama a Premier: Benjani Dan wasan tawagar Zimbabwe, Benjani ya makara zuwa Etihad domin ya saka hannu kan yarjejeniyar komawa Manchester City, bayan da bacci ya kwashe shi […]

Ethiopian Airlines na son karbe iko da Arik Air

Ethiopian Airlines na son karbe iko da Arik Air

Kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines na tattaunawa domin duba yiwuwar karbe ragamar gudanar da kamfanin Arik Air na Najeriya wanda ke fama da matsaloli. Gwamnatin Nigeria ta karbe ragamar gudanar da kamfanin a farkon bana bayan da ya sanar da yin gagarumar asara. Wani babban jami’i a kamfanin Esayas Woldemariam, ya shaida wa kamfanin […]

Alhazan Nigeria bakwai sun mutu a Saudiyya

Alhazan Nigeria bakwai sun mutu a Saudiyya

Wasu alhazan Najeriya bakwai sun mutu a Saudiyya gabanin a fara aikin Hajji.Alhazan sun fito ne daga jihohin Kwara, da Katsina da Kogi da kuma Kaduna. Sannan wata Hajiya daga Jihar Kogi ta Haihu a Madina. Shugaban NAHCON Abdullahi Mukhtar, ya ce za a hukunta jihar da matar ta fito ta hanyar rage mata kujeru […]

Zamu Cigaba Da Gwajin Makamanmu – Jong-Un

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya yi alkawarin gwajin Karin makamai masu linzami ta kan sararin samaniyar Japan, yana mai cewa gwajin baya somin tabi ne.

Zamu Cigaba Da Gwajin Makamanmu – Jong-Un

Kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito shugaban na cewa nan gaba za a samu karin gwaje-gwajen makamai masu linzami, tare da danganta gwajin da suka yi a ranar talata a matsayin shirin yadda za a murkushe Guam domin mayar da martini ga atisayen da sojin Amurka da Koriya ta kudu ke yi. Wannan shi ne […]

Mutane 5 Sun Mutu Sanadiyyar Ambaliyar Ruwa A Birnin Mumbai

Ruwan saman ya tsagaita a yau Laraba a Mumbai, amma kwararru a fannin yanayi sun yi gargadin cewa ta yiwu ya dawo nan da sa’o’i 48.

Mutane 5 Sun Mutu Sanadiyyar Ambaliyar Ruwa A Birnin Mumbai

A kasar India, akalla mutane 5 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa da guguwa suka haddasa a Mumbai, babban birnin kasar, a cewar jami’an gwamnati yau Laraba. Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ya sa komai ya tsaya cik a birnin jiya Talata, wanda ya hana zirga-zirga a kan tituna kuma ya sa […]

Ko Liverpool za ta sayar da Coutinho?

Arsenal za ta iya sayar da dan wasan gaba, Alexis Sanchez, mai shekara 28, idan yarjejeniyar ta yi mata kyau, in babban wakilin Daily Mirror kan kwallon kafa, John Cross.

Ko Liverpool za ta sayar da Coutinho?

Tottenham ta kusa sayan dan Ajentina mai shekara 19, Juan Foyth daga Estudiantes kan kudi fam miliyan 8 kuma tana sake kokarin kammala cinikin Serge Aurier kan kudi fam miliyan 23, in ji Guardian. Liverpool ta yarda ta sayar da dan wasan Brazil mai shekara 25, Philippe Coutinho, ga Barcelona a wata yarjejeniyar da ta […]

MDD ta Gargadi Venezuela Kan Take Hakkin Bil’adama

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa karuwar take hakkokin bil’adama a Venezuela na kawo nakasu ga Demokradiyyar kasar. Gargadin Majalisar Dinkin Duniyar dai na zuwa ne a dai dai lokacin da sabuwar majalisar dokokin kasar ke sanar da fara tuhumar jagororin adawar kasar kan cin amanar kasa.

MDD ta Gargadi Venezuela Kan Take Hakkin Bil’adama

Majalisar wadda ta sanar da amincewa da dokar da wadda za ta fara tuhumar jagororin adawar a yau Laraba, ta ce hakan zai kawo karshen mara bayan da jagororin adawar ke yi ga takunkumin Amurka kan kasar. Duk da cewa, bayanai dangane da sabuwar dokar basu fito karara sun fayyace jagororin adawar da Majalisar za […]

1 2 3 43