Kotu Ta Amince Gwamnati Ta Rike Kudaden Diezani

Biyo bayan karar da hukumar EFCC ta shigar yanzu wata kotun Legas ta tabbatarwa gwamnatin tarayyar Najeriya mallakar kudaden da aka gano tsohuwar ministar man fetur Alison Madueke ta wawure

Ranar 9 ga wannan watan ne Justice Chuka Obiozo na kotun tarayya dake Legas ya zartas da hukumci na wucin gadi da ya mallakawa gwamnatin tarayya makudan kudaden da aka gano su cikin bankin Stirlin.

Hukumcin alkalin ya biyo karar da hukumar EFCC ta shigar ne. A hukumcin farko alkalin ya umurci bakin ko kuma ita ministar ko wanda ya san ya mallaki kudin ya gurfana a gaban kotun tare da sheidu cikin makonni biyu. Sai dai bayan makonni biyu babu wanda ya je kotun saboda haka kotun ta mallakawa gwamnati kudaden na dindindin

Ita hukumar EFCC ta tabbatarwa kotun cewa kudaden mallakar tsohuwar Minista Alison Madueke ne da aka kyautata zaton ta wawuresu ne daga hukumar matatar man fetur ta kasa NNPC a shekarar 2014.

Hukumar EFCC ta zargi tsohuwar ministar da ajiye kudaden a bankuna guda uku. Sai dai tun a watan Fabrarirun bara alkali Musiliu Hassan na kotun tarayya ya amince da karbe kudaden dake sauran bankunan guda biyu.

Kudaden da kotun ta mallakawa gwamnatin tarayya sun hada da N23.4bn da wasu N9bn.

A Wata Majiyar Kuma

Alkali Abdulaziz Anka, yace kudin ya zama mallakar gwamnatin Najeriya gaba daya kamar yadda Hukumar EFCC ta bukata.

Wannan hukunci ya zo ne kwanaki, bayan da Alkali Anka ya bada umurnin karbe jimillar gidaje 56, da tsohuwar ministar ta mallaka.

Kimanin watanni uku da suka gabata ne dai aka rawaito tsohuwar ministar man na cewa a shirye ta ke ta fuskanci hukuncin zaman gidan yari, bayan ta tona asirin wadanda suka hada kai wajen yashe kudaden al’ummar Najeriya.

Karanta:  Gwamna Tambuwal ya yi wa mutumin da matarsa ta haifi 'yan hudu goma ta arziki
Asalin Labari:

VOA Hausa

824total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.