A bayyana Odinga a matsayin ‘Shugaban Kasa’ – ‘Yan adawar Kenya

Kasashen Burtaniya da Amurka sun bi sahun kasashen waje ‘yan sa ido na Kungiyar tarayyar Turai, Kungiyar Hadin kai ta Afirika, Kungiyar kasashe rainon Ingila da kuma Cibiyar Carter wajen kira ga shugabannin jam’iyyu da su kara hakuri da kuma kaucewa duk wani abu da zai harzuka fitina, kafin fadin babban sakamakon zabe da ake tsammani ranar Juma’a.

‘Yan adawa na kasar Kenya a ranar Alhamis, sun bukaci da a bayyana dan takararsu Raila Odinga a matsayin sabon shugaban kasa, ta hanyar fatali da sakamakon da ya nuna cewar shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya sha kansa a zaben, yanayin da ke neman jefa rudani ga kasashen Afirika ta gabas.

Shagulgulan murna sun barke a yankunan da ‘yan adawa suka fi rinjaye, a yayin da a gefe daya kuma suka yi zanga-zangar kin nuna amincewa da magudin zabe da Odinga ke zargin an aikata. Kasar dai, ta taba shiga halin rudani da hayaniya a zabukan da aka gudanar a 2007 da 2013.

 

 

 

 

Asalin Labari:

Daily Nigerian, Muryar Arewa

464total visits,1visits today


Karanta:  Kenyatta Ya Amince Da Hukuncin Kotun Koli

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.