A Kano ‘Yan Najeriya Sun Yi Tsokaci Kan Dawowar Buhari

Mutanen Kano da suka yi furuci sun yi tsokaci akan yajin aikin malaman jami'a da sha'anin tattalin arziki da tabarbarewar tsaro da rabuwar kawuna tsakanin bangarorin gwamnati da majalisa da na shari'a.

Wadda ta fara magana tace abun da ya fi mahimmanci shi ne shugaban ya huta ya murmure da kyau kana ya maida hankali kan matsalolin jami’o’i domin malamansu dake yajin aiki yanzu su koma.

Shi ko Yusuf Lawal Babale fata ya yi shugaban kasa ya maida hankali akan harkar tsaro da tattalin arziki tare da hada kawunan jama’a.

Baicin ‘yan Najeriya da suka yi tsokaci kungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da bayyana ra’ayinsu dangane da alkiblar da ya kamata shugaban ya kalla a yanzu.

Kwamred Nura Iro Ma’aji jami’i ne a kungiyar dake bibiyar ayyukan majalisun dokoki da shugabanci nagari yana mai cewa sun yi magana ya kamata shugaban kasa ya fitar da wata matsaya akan fadi in fada da bangarorin kasar suke ta yi. Haka kuma bayan ya bar kasar harkokin ta’addanci sun sake farfadowa. Haka ma sace sacen mutane a kasar ke yaduwa.

Ma’aji ya jaddada mahimmancin dangartaka tsakanin bangarorin zartaswa da na majalisa da shari’a. Bai kamata shugaba ya bar rabuwar kawuna tsakaninsu ta samu tushe lokacin da yake mulki ba, injishi. Ya kamata a zauna a gayawa juna gaskiya.

Yanzu malaman jami’o’i sun kwashe mako guda suna yajin aikin “sai baba ta gani”. Farfasa Mahmud Lawal shugaban kungiyar malaman reshen shiyar arewa maso yammacin kasar yana cewa suna farin cikin dawowar shugaban kasa.

A kungiyarsu ta malaman jami’o’i suna kallon gwamnati a matsayin abu mai cigaba kullum kuma duk wani abu da aka faroshi duk wanda ya zo mulki zai dora a kai sai a ci gaba.

Yace sun yi yarjejeniya da gwamnatin baya. Sun yi zaton gwamnatin da ta zo zata aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma amma hakan bai samu ba har suka shiga yajin aikin.

Karanta:  Sojin Najeriya zasu fadada atasaye zuwa Kudu maso yammacin kasar

Suna fatan dawowar shugaban wani abu mai mahimmanci zai faru domin su koma bakin aikinsu dalibai kuma su koma karatu.

Asalin Labari:

VOA Hausa

626total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.