A Naija an gano wasu biliyoyin kudi da aka wawure

Gwamnatin jihar Neja a Nigeria ta ce ta gano Naira milyan Dubu 6 da Milyan dari 2 na yan fansho da aka sace a jihar musamman daga ma’aikatan Kananan Hukumomi da Ma’aikatar Ilimi ta jahar. Yayin da hakan ke faruwa kuma Kungiyar Kwadagon jijhar ta koka kan rashin biyan hakkokin tsaffin Ma’aikatan da kudaden Paris kulop da jahar ta samu.

Mukaddashin Gwamnan jahar Alhaji Ahmad Muhammad Getso, wanda ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki kan batun fansho na jahar,ya ce an yi kwana da wadannan kudaden ne ta wajen fakewa da wani sabon tsarin fansho na jahar tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, wanda y ace wannan ne babban dalilin da ya sa ‘yan fanshon jahar su ka shiga matsala.

To saidai kuma kungiyar Kwadagon jahar ta yi watsi da lamirin taron kwata-kwata. Ta ce hatta ita kanta gwamnati mai ci ta ki amfani da kudaden Paris Kulub wajen biyan hakkokin tsoffin ma’aita. Kwamrad Yahaya Idiris Ndku, Shugaban Kungiyar Kwadagon jahar ta Naija, ya ce an baiwa jahar kasonta na Paris Kulob har sau biyu amma ta ki biyan tsoffin ma’aikata hakkokinsu.

Asalin Labari:

VOA Hausa

451total visits,2visits today


Karanta:  Mayakan Saman Najeriya Sun Rugurguza Sabbin Sansanonin Boko Haram a Dajin Sambisa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.