Aikin Hajji: Mahajjata 2 ‘Yan Kano Sun Mutu A Saudi Arabia

Mahajjata biyu daga Jihar Kano sun rasa ransu yayin gudanar da aikin hajjin bana a Saudi Arabia, a cewar Hukumar Alhazai ta Jihar ranar Alhamis.

Shugaban Sashin Hurda da Jama’a na ma’aikatar Alhaji Nuhu Badamasi ne ya sanar ta wayar tarho daga garin na Makkah cewa wadanda suka mutun duka maza ne kuma sun mutu a Makkah yayin da suke gudanar da aikin Hajj a Arafat.

“Mahajjatan biyu da suka rasa ransu yayin gudanar da aikin Hajjin bana sun mutu ne a Makkah bayan gudanar da ginshikin aikin Hajjin wato tsayuwar Arafat,” a cewarsa.

Badamasi ya ce wanda suka riga mu gidan gaskiyar sun fito ne daga kananan hukumomin Dala da Doguwa, haka kuma tuni akayi jana’izarsu a garin na Makkah kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

A shirye-shiryen da ake na dawo da Alhazan gida Nijeriya, Badamasi cewa yayi za a fara dawo dasu ne ranar 15 ga watan Satumba nan da muke ciki.

Yace da yawa daga cikin mahajjatan sun ziyarci Madinah, sauran da basu samu zuwa ba kuma ana nan ana shirin zuwansu daga Makkah.

Kakakin Ma’aikatar Alhazan ya kara da cewa “Kusan dukkan mahajjatanmu sun ziyarci Madinah face 15 daga cikin jami’an mu wanda suma ana nan ana shirin zuwansu daga nan kuma a dawo dasu gida.”

Kusan Alhazai 5,500 ne daga Kano suka gudanar da aikin Hajjin bana

(NAN).

498total visits,1visits today


Karanta:  Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.