Alhassan Ta Halarci Taron Majalisar Zartarwa Tare Da Buhari

Ministan Mata, Aisha Alhassan na daga cikin mahalarta taron Majalisar Zartarwa na Gwamnatin Tarayya da ake gudanarwa yau din nan.

Ta isa gurin taron dake fadar shugaban kasa da misalin karfe 10:45 na safe.

Taron da ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai jagoranta za a fara shi ne da misalin karfe 11:00 na safe.
Alhassan a wata hira da tayi da sashin Hausa na BBC satin da ya wuce ta bayyana cewa zata marawa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar baya a zaben shugaban kasa mai zuwa na shekarar 2019 ba Shugaba Muhammadu Buhari ba.

“Atiku shi ne uban gida na tun kafin in fara siyasa, haka kuma Baba Buhari bai fada mana cewa zai yi takara a shekarar 2019 ba. Kai bari ma in fada maka a yau din nan cewa koda Baba yace zaiyi takara a shekarar 2019, na rantse da Allah zanje gabansa in durkusa in fada masa cewa Baba nagode da damar da kabani a gwamnatinka a matsayin minister. Amma Baba kamar yadda ka sani zan marawa Atiku baya ne kawai saboda uban gida na ne,” a cewarta.

Haka kuma ministan ta fadawa manema labara na gidan gwamnati cewa bata tsoron rasa aikinta, inda take cewa “Allah ne Mai bayarwa kuma Mai karbewa. Shi kenan kawai. Ka sani cewa komai nada karshe.”

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

737total visits,1visits today


Karanta:  Atiku: APC Ta Musanta Cewa Ta Bukaci Alhassan Da Tayi Murabus

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.