Alhazai Na Fuskantar matsaloli iri daban-daban A Mina

Ana daf da fara dawo da Alhazan Najeriya, Alhazan ke fuskantar matsalolin iri daban-daban da suka hada da wurin kwana da kuma wurin kewaya wa.

Yayin da ake haramar dawowa daga aikin Hajjin bana, Alhazan Najeriya dake Mina suna fuskantar matsalolin wurin kwana da kuma wurin kewayawa.

Wannan yasa wasu da yawa suke kwana waje, yayinda wasu da yawa kuma sai sun shiga dogon layi kafin su samu damar kewaya wa.

Wannan lamarin ya fito fili ne lokacin da shugaban hukumar Alhazan Najeriya Barister Abdullahi Mukthar Mohammed ya zagaya wurin kwanan Alhazan domin ganin halin da suke ciki.

Jihohin da abin yafi shafa sun hada da Kaduna, Kano, Sokoto da Bauchi.

Imam Hussaini Tsoho shine shugaban Alhazan jihar Kaduna kuma ya shaidawa wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El-Hikaya cewa, wasu Alhazan ma basu da ko katifan kwanciya sai sun dauko dardumar da aka shinfida cikin tanti sun fito waje sun shinfida.

Haka kuma Imam Tsoho yayi korafi gameda bukatar samarda makewayin mata daban, na maza dadan.

Asalin Labari:

VOA Hausa

506total visits,4visits today


Karanta:  'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 11 a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.