Tarihin Ali Nuhu

Ali Nuhu Mohamamed wanda aka haifa a ranar sha biyar ga watan Maris na alif dari tara da saba’in da hudu (15 March 1974), Jarumi ne na fina-finai da suka hada da na Hausa da kuma Turanci, sannan kuma ya kasance mai bada umarni wajen shirin fina-finan Hausa, yakan taka rawa da kuma rubuta fina-finai. Jarumi Ali Nuhu yayi fice a matsaki daban-daban wnda ma wasu da dama kan kalle shi a matsayin kwarzo kuma haziki wanda ya dauki lambobi yabo dana girma da suka haura na duk wasu Jarumai a cikin masana’antar ta fina-finan Hausa.

Ali Nuhu ya kasance Jarumi na farko da ya fara fitowa a fina-finan kudancin Najeriya wanda a cikin su suka hada da “Sitanda” da kuma “Last Fligh to Abuja”. A lokutan fitowar sa a cikin wadansu fina-finai na Turanci, Jarumi Ali ya samu suka daga bangarorin al’umma musamman ma ta yadda yakan yi dabi’u da suka sabawa al’adar Hausa wacce ya fito daga bangaren ta.

Kuruciya, Rayuwar Gida da ta ‘Yan Uwa

Ali Nuhu da matarsa Maimuna Ja-AbdulKadir

An haifi Jarumi Ali Nuhu a garin Maiduguri dake cikin jihar Borno a Najeriya. Mahaifinsa mai suna Nuhu Paloma ya fito ne daga shiyar Balanga ta jihar Gombe a Najeriya. Mahaifiyarsa Fatima Karderam Digema ta fito ita kuma daga shiyar kauyen Bama a jihar Borno.

Nuhu yayi mafi yawan shekarun sa na kuruciya a birnin Kano. Ya halarci makarantar firamare ta Riga da ma makarantar Sakandare duka a jihar Kano. Nuhu ya kasance mai rike da takardun digiri daga Jami’ar Jos inda ya karanta ilimin kasa (Geography).

Ali ya samu halartar wadansu makarantu inda yayi gajeren karatu domin koyar fannin shirin fim. A cikin wadan nan makarantu akwai Jami’ar Kudancin Califonia dake kasar Amurka.

Jarumi Nuhu ya kasance yana da aure inda yake tare da matarsa mai suna Maimuna Ja-AbdulKadir inda suka da ‘ya’yansu biyu da suka haka da Fatima da kuma Ahmad.

Kasancewa Jarumi
Jarumi Ali Nuhu ya shiga masana’antar shirya fina-finai a shekarar alif dari tara da casa’in da tara (1999) wanda yayi fice a cikin wani shirin fim mai suna Sangaya. Jarumi Ali ya samu kansa a cikin shirin fina finai masu dumbin yawa wadanda akalla yawansu ya haura 300. Fina finan Jarumi Ali na yaren Hausa sunfi yawa. Sai dai bangaren na Turanci ma ba’a barshi a baya inda ya fito a fina finai masu yawa ciki harda shahararren fim fin nan mai suna Sitanda.

Kadan daga cikin fina finan Ali Nuhu

Year Title Role Genre Production Company
2007 Sitanda Actor Drama
2011 Carbin Kwai Actor Drama
2012 Madubin Dubawa Actor Drama
2012 Last Flight to Abuja Actor Drama Nollywood Film Factory
2013 Blood and Henna Actor Drama Newage Networks
2013 Confusion Na Wa Actor Drama Cinema KpataKpata
2013 Wani Hanin Actor Drama
2014 Matan Gida Actor Drama
2015 Jinin Jikina Actor Drama
2016 Nasibi Actor Drama
2016 Ojukokoro Actor Drama Singularity Media
2017 Banana Island Ghost Actor Drama

Lambar Yabo da ta Girma
Ali Nuhu ya kasance Jarumi na farko wanda ya samu karbar kyaututtuka mafi yawa a cikin masana’antar Kannywood. Ali Nuhu ya fara samun kyautar lambar yabo a shekarar dubu biyu da biyar (2005) a cikin shirin fim din Razani wanda ya samu Gwarzon Jarumi.

Shekara Lambar Yabo Fanni Fim Sakamako
2005 Arewa Films Award Gwarzon Jarumi Razani Won
2007 3rd Africa Movie Academy Awards Best Upcoming Actor award Sitanda Won
2008 The Future Award Gwarzon Jarumi Won
2011 Zulu African Film Academy Awards Best Indigenous Actor Carbin Kwai Won
2012 Best of Nollywood Awards Gwarzon Jarumi (Hausa) Madubin Dubawa Won
2013 9th Africa Movie Academy Awards Best Actor in a supporting role Blood and Henna Nominated
2013 Nigeria Entertainment Awards Gwarzon Jarumi Confusion Na Wa Won
2013 Best of Nollywood Awards Gwarzon Jarumi (Hausa) Wani Hanin Won
2013 City People Entertainment Awards Fuskar Kannywood Won
2014 Kannywood Awards Gwarzon Jarumi Matan Gida Won
2014 Leadership Awards Best Artiste Won
2014 City People Entertainment Awards Gwarzon Jarumi Won
2014 City People Entertainment Awards Recognition Award Won
2014 Arewa Music and Movie Awards Pride of Kannywood Won
2014 Arewa Music and Movie Awards Gwarzon Jarumi Popular Choice Award Won
2015 19th African Film Awards Best Outstanding Actor Afro Hollywood Awards Won
2015 Best of Nollywood Awards Gwarzon Jarumi (Hausa) Jinin Jikina Won
2015 Kannywood Awards Gwarzon Jarumi Popular Choice Awards Won
2015 City People Entertainment Awards Jarumi na Musamman a Kannywood Won
2016 Best of Nollywood Awards Gwarzon Jarumi (Hausa) Gamu nan dai Won
2016 Arewa Music and Movie Awards Gwarzon Jarumi Nasibi Won
2016 Kannywood Awards Gwarzon Jarumi Nasibi Nominated
2016 City People Entertainment Awards Fuskar Kannywood Won
2016 Arewa Creative Industry Awards Kyauta ta Nishadi Won
2017 Northern Nigeria Peace Awards Gwarzon Shekara na Arewacin Najeriya Won

Shafukan Sada Zumunta
Website: http://www.alinuhu.net/
Twitter: Ali Nuhu
Facebook: Ali Nuhu
Instagram: Ali Nuhu
Wikipedia: Ali Nuhu

Shafuka masu alaka: Tarihin Hadiza Gabon

3431total visits,1visits today