Alkali ya Yarharbi Wani ɗan Bindiga

Wani alkali a cikin jihar Ohio ta Amurka ya ɗirka wa wani ɗan bindiga harsasan da suka jikkata shi a wani harin kwanton bauna da ya faru a wajen kotu

An harbi mai shari’ah Joseph Bruzzese Jr sau da dama da safiyar ranar Litinin a yankin Steubenville, inda shi ma ya mayar da martani.

Jami’in ‘yan sanda Fred Abdalla ya fada wa manema labarai cewa maharin da alkalin sun yi musayar wuta, inda kowannensu ya yi harbi kimanin sau biyar.

Shi ma wani jami’in tsaron kutun ya yi harbi da dama kan mutumin da ake zargi.

Mai shigar da kara a shiyyar Jefferson ta bayyana maharin a matsayin Nathaniel Richmond, amma ta ce ya zuwa yanzu ba su gano manufar da ta sa ya far wa alkalin ba.

Mista Richmond shi ne mahaifin Ma’Lik Richmond, wani dan kwallon kafa da hukuncin samunsa da aikata fyade ya shiga kanun manyan jaridun Amurka a 2012.

Mai gabatar da karar Jane Hanlin ta ce babu wata alaka tsakanin mai shari’ah Bruzzese da wannan shari’ah ta aikata fyade.

An dauki mai shari’ah Bruzzese, wanda ke shari’ah tun a shekarar 1998 a kotun yankin Jefferson, cikin jirgin sama zuwa asibiti a Pittsburgh don yi masa tiyatar gaggawa.

Sheriff Abdalla ya ce shi ne ya ba alkalin mai shekara 65 shawara tsawon shekaru da dama a baya cewa ya dinga yawo da bindiga.

“Wannan mutum kawai ya zo ya labe yana jiran isowar alkalinmu,” jami’in ‘yan sandan ya fada wa manema labarai bayan sa’o’i da harbe-harben.

“Abin takaici ne. Da sanyin safiyar ranar Litinin.”

“Ga alkali, an harbe shi a gaban kotunsa, abin ya tayar min da hankali. Wannan kwanton bauna ne da yunkurin kisa.”

‘Yan sanda sun kuma tsare direban da ya kawo mahari a mota, ko da yake, sun ce sun yi imani bai san abin da fasinjansa ke shiryawa ba.

Asalin Labari:

BBC Hausa

903total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.