Al’umman Igbo Sun Yi Na’am da Janye Shirin Korarsu daga Arewacin Najeriya

A watan Mayu ne gamayyar kungiyoyin matasan arewa suka ba 'yan kabilar Igbo dake zaune jihohin arewa har zuwa daya ga watan Oktoba su koma yankinsu, yankin da Nnamdi Kanu yake neman ya balleshi daga tarayyar Najeriya ya kafa kasar Biafra

‘Yan kabilar Igbo dake arewacin Najeriya sun yi na’am da matakin da gamayyar kungiyoyin matasan arewa suka dauka na janye shirin korarsu daga jihohin arewa kafin daya ga watan Oktoba na wannan shekarar.

Da dama daga cikin mutanen Igbo suka yanke shawarar cigaba da zamansu a arewa kafin janyewar. Amma sun ce matakin ya faranta masu rai tare da kwantar da hankalinsu.

Okechukwu Nnamdi dan kabilar Igbo da ya kwashe fiye da shekaru 30 yana Sokoto yana mai cewa gabansa bai taba faduwa ba bisa sanarwar ta farko. Yace ko an ce a koma shi bashi da niyyar komawa.Yace Sokoto ta zama masa gida. Yace Allah ya sa kabilu daban daban saboda haka yaya wani zai tashi ya ce kabilar Igbo su tashi wai domin ana kwararsu.

Saidai wasu na ta’allaka sauyin matsayin matasan arewa da dawowar shugaban kasa. Da can rashin dawowarsa ya jefa kabilar Igbo cikin fargaba. Wani Friday yace lokacin da aka yi sanarwar kowa ya ji tsoro. Ko yanzu ma da suka janye akwai sauran tsoro garesu, su mutanen Igbo. Wata tace jawabin shugaban kasa farkon makon nan ya kwantar da hankalinsu.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1992total visits,1visits today


Karanta:  Buhari ya yi alla-wadai da harin mujami’a a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.