Ambaliyar Ruwa Mafi Muni a Afirka a Shekara 20

Birnin Freetown din Saliyo ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa da aka dade ba a ga irin ta ba cikin shekaru masu yawa, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, yayin da wasu daruruwan suka rasa muhallansu.

Wannan ambaliyar ruwa ita ce mafi muni da aka fuskanta a nahiyar Afirka cikin shekara 20.

Ga dai jadawalin wuraren da ambaliayr ruwa mafi muni ya taba shafa a Afirka;

Bala’in sauyin yanayi na El Nino a yammacin Afirka

Daga watan Oktobar 1997 zuwa Junairun 1998, fiye da mutum 6,000 ne suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa da guguwar sauyin yanayi ta El Nino suka shafa a kasashen Somaliya, da Habasha, da Kenya, da Tanzaniya, da Uganda.

A kasar Somalia mutum 1,800 ne suka mutu, wasu 230,000 suka rasa muhallansu a lokacin da tekunan kasar suka yi ambaliya a ranar 18 watan Oktoba.

Ambaliyar ruwan da ta fadawa Algeriya

A ranar 10 ga watan Nuwamba shekarar 2001, mutum 764 sun mutu, wasu 125 kuma sun bace sakamakon ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ya haddasa a birnin Algiers.

Ambaliyar ta hallaka mutum 713, yawancinsu mazauna kusa da wata unguwa mai suna Bab el-Oued da ke gabar teku.

 

Ibtila’in ambaliyar ruwa a Mozambique

Tun daga watan Fabrairu zuwa Maris na shekara ta 2000, kasar Mozambique ta fada wani yanayi saboda ambaliyar da ta fada mata da ta hallaka mutane 699, wasu 95 suka bata, kusan 60,000 suka rasa muhallansu inda suke rayuwa a sansanonin da hukumomin kasar suka kafa.

Ambaliyar ta fi shafar yankin Zambezie, inda mutum 160 suka hallaka, wasu 177,000 suka rasa gidajensu. A makwabciyarta wato Malawi, ambaliyar ta hallaka mutum 176, yayin da 153 suka bace, sai kuma mutum 200,000 suka rasa muhallansu.

Ambaliyar ruwa a Habasha

A watan Agustar 2006, mutum 639 ne wata ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Habasha. A nan ma wasu mutum 35,000 sun rasa gidajensu, ambaliyar ta shafi mutum 200,000 a kudanci, da arewaci da kuma gabashin kasar.

Karanta:  'Yan Ghana Sun Yi Zanga-Zanga Kan Musgunawa Musulman Rohingya

Damunar shekarar 2010

Ambaliyar ruwan da aka fuskanta a 2010 saboda yanayin damuna da aka shiga mai marka-marka, daya ne daga cikin lokutan da ba za a taba mantawa da shi ba a nahiyar Afirka.

A kalla mutum 377 ne suka hallaka, wasu miliyan daya da rabi suka rasa muhallansu a yammacin Afirka.

Kasashen da abin ya fi shafa sun hada da jamhuriyar Nijar inda mutum 118 suka rasu, kasar Ghana kuma mutum 52, sai Sudan mutum 50, da Jamhuriyar Benin mutum 50, kasar Chadi mutum 24, sai kuma Mauritania mutum 21.

Ita kuwa Burkina Faso mutum 16 ne suka mutu, sai a Kamaru kuma mutum 13, a karshe sai kasar Gambia mai mutum 12.

Iftila’in da kusurwar Afirka ta fuskanta a shekarar2006

Daga watan Oktoba zuwa Nuwamba shekarar 2006, mamakon ruwan da aka yi ta shekawa kamar da bakin kwarya, ya afkawa kasar Somaliya inda mutum 140 suka rasu, yawancinsu igiyar ruwa ce ta janye su, wasu kuma Kada ya hallakasu, yayin da hukumomi suka ce wasu sun rasa ransu sakamakon annobar cutar zazzabin cizon sauro.

Haka kuma kasar Kenya ta samu kanta cikin ibtila’in ambaliyar ruwan da mutum 114 suka hallaka, sai kuma kasar Habasha da mutum 80 suka rasu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1485total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.