Ambaliyar ruwa ta hallaka mutum 200 a India

Mummunar ambaliyar ruwan da ta afkawa wasu yankunan jihar Gujarat a kasar Indiya ta hallaka sama da mutum 218, kamar yadda jimi'an gwamnati suka tabbatar.

Kwanaki biyu da yin ambaliyar ruwan, aka sake gano wasu karin gawawwakin sama da mutum 100.

Jami’an jihar sun tabbatar da cewa, ambaliyar ruwan ta shafi a kalla mutum 450,000.

A bana kadai jihohi 20 ne suka fuskanci ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na kasar Indiya.

Haka kuma a arewa maso gabashin jihar Assam ma an fuskanci ambaliyar inda mutane da dama suka mutu, wasu daruruwa suka rasa muhallansu.

Gwamnatin Indiya ta sanar da cewa za ta aike da kayan agaji ga wadanda lamarin ya rutsa da su, kuma tuni Firai minista Narendra Modi ya sanar da kai ziyara jihar Assam a ranar Talata, domin jajantawa al’ummar yankin.

Ya kara da cewa makasudin kai ziyarar shi ne samar da maslaha ta dindindin da jihar Assam ke fuskanta a ko wacce shekara.

Kamfnanin dillancin labaran Indiya ya ambato wani jami’in gwamnati na cewa yawancin mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa a jihar Gujarat sun fara komawa kauyukansu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

733total visits,8visits today


Karanta:  An Zargi 'Yan Rohingya Da Kashe 'Yan Hindu

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.