Amnesty Ta Bukaci Ayi Inciken Bacewar Mutane a Najeriya

Yayin da yau ake bikin ranar magance bacewar mutane ta duniya, kungiyar Amnesty International ta bukaci Gwamnatin Najeriya ta gaggauta binciken mutanen da suka bace ta hanyar tursasawa.

Sanarwar da kungiyar ta rabawa manema labarai ta nuna cewar daruruwan mutane da jami’an tsaro suka kama kan wani zargi musamman a Yankin arewa maso gabashin Najeriya sun bata, kuma ‘yan uwansu sun kasa gano inda suke kuma babu wani bayani da akan makomarsu.

A cikin sanarwar, Amnesty ta ambaci ikirarin da mabiya Shi’a a Najeriya suka yi cewa mabiyansu kusan 600 sun bace wadanda ba san inda suke ba bayan rikicin da ya faru tsakaninsu da Sojin kasar a garin Zaria a watan Disemban 2015.

Kungiyar ta ce ‘yan uwan wadanda suka bace sun rasa inda zasu je domin ganin an bi musu hakkinsu.

Sanarwar da Manajan yada labaran kungiyar a Najeriya Isa Sanusi ya rabawa manema labarai ta bukaci gwamnatin Najeriya ta gudanar da bincike kan irin wadannan zarge zarge.

Majalisar Dinkin Duniya ce dai ta ware wannan rana ta 30 ga watan Agusta domin bikin bacewar mutane da ba a san ko dai wadanda hukumomi suka kame ba bayanin dalilin kama su ko kuma kungiyoyin masu dauke da makamai sun yi awon gaba da su.

Mista Sanusi ya shaidawa RFI Hausa cewa suna amfani da wannan rana domin janyo hankalin duniya kan cewa akwai iyalai da dama da suka shafe shekaru cikin damuwa ba su san halin da ‘yan uwansu suke ciki ba.

Asalin Labari:

RFI Hausa

363total visits,3visits today


Karanta:  Buhari Ya Yi Kuskure da Korar Abdulrasheed Maina Daga Aiki -Lauya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.