Amurka ta Sanyawa Kamfanonin Rasha da Chana Takunkumi

A baya-bayan nan ne dai shugaban na Amurka ya yabawa Kim Jun-Un kan matakin daya dauke na dakatar da shirin harba wani makami mai linzami zuwa yankin Guam na Amurka

Kasar Amurka ta sanyawa wasu kamfanonin kasashen Rasha da Chana 16 takunkumi saboda abinda ta kira goyan bayan shirin nukiliyar kasar Koriya ta Arewa. Takunkumin na daga cikin matakan da Amurka ke dauka na dakile samun kudade ga Koriyar domin ci gaba da gina makamin.

Sakataren Baitulmalin Amurka, Steven Mnuchin ya ce abin takaici ne ga mutane ko kuma kamfanonin da ke Chana da Rasha ko kuma wata kasa dabam su taimaka Koriya ta Arewa domin samun kudin da zata ci gaba da gina makaman kare dangi ko kuma hana zaman lafiya.

Takunkumin ya shafi kamfanonin da ke mu’amala da kwal da wasu ma’adinai da kuma hada- hadar kudade da kasar ta Koriya.

Matakin dai ya biyo bayan cacar bakin da aka samu tsakanin shugaba Donald Trump na Amurka da takwaransa na Korea ta arewa Kim Jong-un bayan gwajin makami mai linzamin da Koriya ta gudanar.

Shugaba Trump ya bukaci taimakon kasar Chana domin ganin ta janyo hankalin Koriya tayi watsi da matakan da take dauka.

2510total visits,1visits today


Karanta:  Macron Ya Mara Baya Ga Masu Kyamar Wariya A Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.