Amurka za ta ladabtar da kwamandan sojan ruwanta

Rundunar sojan ruwan Amurka ta ce za ta ladabtar da matukan jiragenta fiye da 10 saboda yadda sojojin ruwan kasar bakwai suka mutu a cikin wata taho-mu-gama tsakanin jirginsu da wani jirgin ruwan dakon kaya na kasar Philiphines a watan Yuni.

Mataimakin Babban Hafsan Sojan Ruwa, Admiral Bill Moran, ya ce daga yau kwamandan da ke bayar da umarni a jirgin yakin tare da wasu manyan jami’an sojan da ke aiki a jirgin su 2 ba za su sake fita aiki da jirgin ba.

Ya ce yanzu rundunar sojan ruwan ba ta da kwarin gwiwa game da kwarewar kwamandan da sauran jami’an ta jagorantar aikace-aikacen rundunar bayan wannan mummunan hadarin da ya afku a daura da gabar tekun Japan.

An dai samu gawawakin wadanda suka mutun ne a gabar tekun yammacin kasar Japan cikin wuraren kwanansu da suka yi kaca-kaca.

Shi kansa kwamandan da za a ladabtar dai, ya samu rauni a cikin hadarin ta yadda har sai da aka ruga da shi zuwa asibiti da wani jirgi mai saukar ungulu.

Sai dai an yabawa wasu jami’an sojin ruwan da ke aiki a jirgin kan abin da masu bincike suka kira jarumtar da suka nuna wajen kaucewa mutuwar karin mutane.

Asalin Labari:

BBC Hausa

433total visits,1visits today


Karanta:  Ma'aikaciyar British Airways Taci Zarafin 'Yan Nigeria a Bidiyo

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.