An Bukaci Dokar Kwarmata Labarin Safarar Mutane

Hukumar yaki da fataucin mutane ta nemi mahukuntan kasar Najeriya da su samar da dokar da zata ba da daman kwarmata labarin safarar mutane tare da amincewa da bayar da tukwuici kamar yadda ake yi yanzu akan kudaden sata da makwarmata suke taimaka wa ana ganosu.

Kakakin hukumar dake yaki da fataucin ko safarar mutane ta Najeriya Mr Josiah Emerem ya bayyana makasudin samun dokar kwarmata labarin safarar mutane.

Yana mai cewa mutane da dama ba sa iya kai rahoton fataucin mutane kamar yadda a keyi da sauran laifuka. Rashin dokar na takaita ma hukumar samun rahotanni aika aikar da ake tafkawa a kasar.

Dokar kwarmata a bangaren cin hanci da rashawa da zarmiya da yiwa tattalin arziki zagon kasa na samun nasara sosai. Inji kakakin dalili ke nan da hukumarsu ta zabura ta nemi gwamnatin tarayya ta aiwatar da dokar domin a dinga kwarmata bayanai kan masu safarar mutane. Yin hakan zai karfafa ‘yan Najeriya su ji karfin kwarmata wa hukumar bayanai.

Dr Abubakar Umar Kari na Jami’ar Abuja yace matakin zai taimaka gaya wajen dakile fataucin mutane a Najeriya musamman a wasu jihohin kudancin kasar inda ake fita da yara mata waje a tilasta masu shiga karuwanci.

 

Asalin Labari:

VOA Hausa

678total visits,3visits today


Karanta:  'Yan sandan Nigeria: 'Evans yana nan bai mutu ba'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.