An Bukaci Mutane Su Kaucewa Gidajensu a Yamai Saboda Ambaliya

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun bukaci dubban mazauna yankin birnin Yammai da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa su kauracewa gidajensu sakamakon ruwan saman da ake ci gaba da tafkawa a birnin.

Gwamnan Yamai Soumana Ali Zataoua ya shaidawa al’ummar Yankunan da ke fuskantar barazanar ta kafar talabijin da su gaggauta ficewa daga gidajensu.

A karshen mako Katanga ta rufta da weani magidanci da dansa bayan ruwan sama da aka sashe sa’o’I ana makawa a Yamai.

Mazauna kusa da rafin Gountou-Yena a Yamai sun fi fuskantar barazanar ambaliyar, yayin da gidaje sama da 300 suka rushe a Gabagoura.

Tun watan Yuni akalla mutane 41 suka mutu a sassan Nijar sakamakon ambaliyar ruwa.

Asalin Labari:

RFI Hausa

469total visits,1visits today


Karanta:  'Majalisar Dinkin Duniya Ta Gaza Hukunta Dakarunta Kan Laifukan Fyade'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.