An Gurfanar da Malamin Makaranta Saboda Zargisa da Lalata da ‘Yan Mata 3 ‘Yan Uwan Juna

Daga Garin Lagos- Wani Malamin makaranta mai shekaru 23 mai suna Ibrahim Idris ya bayyana a gaban kotun majistire  ranar Talata saboda zarginsa da lalata da ‘yan mata uku ‘yan gida daya. Wanda ake zargin malamin makaranta ne dake koyar da ilimin Arabiya na zaune a gida mai lamba 2, layin Kelani, dake tashar Adealu kusa da garin na Lagas.

Ana dai zargin malamin da cin zarafin yaran. Mai gabatar da qara Sifeto Clifford Ogu ya shaidawa Kotun cewa an aikata laifin ne tun daga watan Mayu zuwa watan Agustan shekarar nan da muke ciki a gidan wanda ake zargin.

Ogu yace ‘yan matan dai ‘yan uwan juna ne da shekarunsu ya kama daga bakwai zuwa 12, inda wanda ake zargin yayi amfani da damar koya musu darasin Arabiya da na Ilimin Addinin Musulunci.

“Iyayen yaran basu san cewa wanda ake zargin na cin zarafin ‘ya’yan nasu ba har sai da suka canza matsuguni zuwa wata unguwar inda suke bukatar canzawa  yaran wata makarantar.

“Karamarsu ce take shaidawa babarsu cewa basa san wani malamin na daban ya rika koya musu darrusan”

Ogu yace da jin wadannan bayanan daga yarinyar, sai uwar yarinyar ta rika yi mata tambayoyi inda yarinyar ta shaida mata duk abubuwan da suka rika faruwa a baya.

“An kai rahotan lamarin ne caji ofis din ‘yan sanda inda ya kai ga tsare wanda ake kara” a cewar Mai gabatar da kara

Wannan laifin dai ya saba da sashe na 137 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Legas na shekara ta 2015. Tuni wanda ake zargin ya musanta zargin da ake yi masa.

Karanta:  'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 a Kan Iyakar Najeriya

Mai Shari’a Mrs Taiwo Akanni ya bada bailin wanda ake zargin kan kudi naira 250,000 tare da masu tsaya masa su 2.

An daga shari’ar zuwa 11 ga watan Satumba, 2017

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

799total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.