An gurfanar da wani mutum a gaban Kotu sakamako kama shi da akayi da kokon kan mutum

Wani mutum dan shekara 30, mai suna Shehu Gidado ya gurfana ranar Talata a gaban Kotun Majistire dake Iyaganku, Ibadan, sakamakon zarginsa da akayi da mallakar kokon kai da kashin kirjin mutum ba bisa ka’ida ba.

Gidado mazaunin sabuwar unguwar Iba dake Okokomaiko a Legos na fuskantar cajin da ya hada da mallakar kokon kashin kan mutum ba bisa ka’ida ba.

Dansanda mai gabatar da kara, Sifeto Sunday Fatola ya fadawa Kotu cewa an kama Gidado 7 ga watan nan na Agusta da muke ciki da misalign karfe 2:30 na yamma a Ogbomoso kan titin Ilori da kokon kan mutum

Dansanda ya kuma ce ana zargin mutumin da mallakar kasusuwan kirazan mutune biyu ba bisa ka’ida ba.

Fatola ya fadawa kotun cewa jami’an tsaro a wajen bincikar ababan hawa, sun tsayar da wata bas motar haya sai suka kama wanda ake zargin dauke da bakar jakar leda tattare da abubuwan da ake zarginsa da su.

“Muna zargin samun sassan jikin mutune a jakar leda mallakar Gidadon ba kuma tare da samun ingantaccen bayanin mallakar su ba”,  Dansandan ya fadawa kotun.

Fatola yace laifin dai ya sabawa sashi na 329 (1) na manyan laifuka na shekara 2000 na jihar Oyo

Alkalin Majistirin, Mr Abdulateef Adebisi, ya bada bailin wanda ake zargin kan kudi naira 200,000 da kuma mutane biyu da zasu tsayawa masa. Sannan ya daukaka karar zuwa 20 ga watan Nuwanba da muke ciki (NAN)

392total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.