An jefe Wani Mutum Har Lahira Sakamakon Aikata Zina

Ranar litinin Din da ta gabata ce ‘Yan Taliban suka jefe wani mutum har lahira saboda cajin sa da akayi da aikata zina da wata mata a lardin Badakshan, na Afghanistan, inji wani jami’in cikin gida.

“lamarin ya faru ne a gundumar Raghistan wanda ke karkashin ikon yan Taliban” kamar yadda Gwamnan Mawlavi Ghulamullah ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Xinhua na qasar Sin

Kodayake bai yi qarin haske kan lamarin da makomar matar da aka aikata zinar da ita  ba

‘Yan Taliban dai sunyi qaurin suna wajen aiwatar da tsauraran hukun-hukunce a bainar jama’a kan waxanda ake zargi da aikata laifuka a guraren da suke da iko da su a qasar.

Har yanzu qungiyar bata ce komai kan lamarin ba (NAN)

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

497total visits,1visits today


Karanta:  An yi harbi kan ofishin jakadancin Israila a Jordan

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.