An Kaddamar da Burodin Kwankwasiyya

Wani kamfanin yin burodi a Najeriya ya kaddamar da wani sabon nau’in burodi a cikin jerin wadanda ya saba yi.

Shi dai wannan burodi mai suna Kwankwasiyya ya samu tagomashi daga bangorin al’umma daban-daban wanda ya hada da jarumai na masa’antar shirya fina finan Hausa mai suna Kannywood a matsayin jakadun burodin Kwankwasiyya.

 

The ambassador’s of kwankwasiyya Bread up up up Kwankwasiyya bread

A post shared by Hussaina Musa (@hussaina_musa_twins) on

Jaruma Hassana ‘Yan Biyu da Usaina ‘Yan biyu sun wallafa a shafin su na Instagram inda bakin kowaccen su ke cike da shi wannan nau’i na burodin Kwankwasiyya.

Bugu da kari Hussani ‘Yan Biyu ta wallafa hotuna kala-kala a shafin na ta na Instagram hotuna na yara da manya masu rike da shi wannan nau’i na burodin Kwankwasiyya.

Kamfanin burodi na Taofeeq ya fitar da burodin Kwankwasiyya a ‘yan kwanakin nan inda ya sanya masa suna “IN THE KWANKWASIYYA WORLD CONTINUE”.

 

We welcome your comment

A post shared by Hussaina Musa (@hussaina_musa_twins) on

Al’umma da dama na bangarori daban-daban a Najeriya tana fitowa da salo kala-kala don nuna goyon bayan su ga tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso gami da kiranye-kiranye da ya sake fitowa takarar shugancin kasa.

Dr Rabiu Kwankwaso wanda yake a halin yanzu Sanatan Kano ta tsakiya daga jihar Kano ya taba yin takara a shekara ta 2014 tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yazo na biyu a zaben fitar da gwani da akayi a birinin Legas inda ya kayar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

1913total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.