An Kama Wadanda Suka Yi Wa Wata Mata Fyade a Mota

An kama wasu mutum hudu a birnin Casablanca, bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna yadda aka ci zarafin wata mata ta hanyar yi mata fyade a motar bas.

Faifan bidiyon, wanda ya bayyana a ranar Lahadi, ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a shafukan sa da zumunta. Ya nuna yadda matasan ke dariya yayin da suke cin zarafin matar.

Kamfanin sufuri na M’Dina Bus ya fitar a wata sanarwa cewa, an kama wadanda suka aikata laifin a ranar Litinin.

Ya kara da cewa, ana bincike a kan hakan.

Wata sanarwa da ‘yan sanda suka fitar ta ce, matar da aka ci zarafin mai shekara 24, tana da matsalar rashin gane abu da wuri, don haka ba a samu wani korafi daga gareta ko direban motar ba har sai da bidiyon ya bayyana.

Kamfanin sufuri na M’Dina Bus ya kare direban motar wanda ake zargi da rashin taimakon matar, inda ya ce: “A wannan gaba, ba za mu iya cewa direban ya gaza taimakon matar ba kamar yadda kafafen sa da zumunta ke yadawa, saboda bidiyon mai tsawon minti daya ba zai iya bayyana dukkan abubuwan da suka faru ba.

Kasa da mako biyu da suka gabata, kafafen yada labarai na Moroko sun ruwaito cewa an ga wani bidiyo inda maza da yawa ke bin wata matashiya da ke tafiya ita kadai a birnin Tangier da ke Kudancin kasar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

694total visits,2visits today


Karanta:  Barcelona: 'Yansanda Sun Harbe Mutum Biyar Da Ake Zargi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.