An kama wani da hannayen mutum a jakarsa

An bayar da rahoton cewa, jami'an tsaro a gabas maso yammacin kasar China sun ga wani abun mamaki da ya razana su, a lokacin da suka kama wani da hannayen mutum zai wuce da su.

Wani bidiyo ya nuna cewar jami’ai ne suka tunkari Mista Zheng mai shekara 50 a tashar mota a Duyun, da ke lardin Guizhou, bayan da aka gano hannayen a wurin da ake yin bincike da na’urar gano abin da mutum yake dauke da shi ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata.

Mai gadin wurin ne ya shaida wa wata kafar labarai cewa, “Na tambaye shi mene ne a cikin jakar, sai ya ce min hannu ne.”

A cewar wata jarida ta Kudancin China, a take ma’aikata suka kama shi, inda ake zargin yana da hannu a kisan.

Ko da yake, Mista Zheng ya yi bayanin cewa ya dauki hannun dan uwansa ne zai tafi da shi, wanda aka yanke masa hannun sakamakon wani hadarin lantarki da ya sameshi.

Mista Zheng ya ce, dan uwansa ne ya bukaci ya taimaka masa ya kai masa hannayen, saboda yayin da ya mutu, a binne gawarsa a wuri daya.

Hukumomi sun sallami Mista Zheng bayan da asibitin da dan uwansa ya yi jinya suka tabbatar da hakan.

A al’adar kasar China sun yi imanin cewa idan mutum ya mutu sai an hada dukkan gabobin jikinsa kafin a binnen shi, ‘don ya kwanta lafiya a kabarinsa.’

Sai dai kuma, yawanci wadanda suka karanta labarin a intanet abin ya kidimasu, kasancewar al’amarin da ya shafi lafiya na bukatar neman izinin tafiya da sassan jikin mutum a kasar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

327total visits,1visits today


Karanta:  Amurka ta Sanyawa Kamfanonin Rasha da Chana Takunkumi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.